-
Somaliya Ta Kori Wani Babban Jami'in MDD
Jan 02, 2019 05:16Gwamnatin Somaliya ta umurci wakilin majalisar dinkin duniya a kasar da ya fice daga kasar, bisa zarginsa da shishigi a cikin al'amuran kasar.
-
Jam'iyyun Adawa A Kasar Sudan Sun Yi Kira Da A Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa
Jan 02, 2019 03:46A wani bayani da jam'iyyun siyasar su ka fitar sun bukaci ganin an kafa majalisar rikon kwarya wacce za ta sami wakilcin jam'iyyun siyasar kasar domin fita daga halin da kasar take ciki
-
Moroko: An Rusa Wata Kungiya Mai Fataucin Mutane
Jan 02, 2019 03:44'Yan Sandan kasar Moroko sun sanar da rusa wata kungiyar masu fataucin mutane a kusa da birnin Ribat
-
Congo: An Dakatar Da Allurar Rigakafin Ibola Saboda Rashin Tsaro
Jan 02, 2019 03:42Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta sanar da dakatar da allurar rigakafin saboda rikice-rikicen da su ka kunno kai sanadiyyar zabe
-
Libya: An Kwato Mutanen Da 'Yan Ta'adda Su Ka Yi Garkuwa Da Su
Jan 02, 2019 03:40Kakakin sojan kasar Libya ya sanar a jiya Talata cewa; Sojojin kasar sun yi nasarar kwato da mutane 21 da 'yan ta'adda su ka yi garkuwa da su
-
Mahara Sun Kashe Mutane Fiye Da 30 A Tsakiyar Kasar Mali
Jan 02, 2019 03:38Gwamnatin kasar Mali ta sanar a jiya Talata cewa wasu mutane masu dauke da makamai sun kai hari a kauyen Koulogon da yake a yankin Mopti a tsakiyar kasar
-
Somaliya Ta Kori Wakilin Majalisar Dinkin Duniya
Jan 02, 2019 03:36Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Somaliya ta bayyana wakilin majalisar Dinkin Duniya a kasar, Nicholas Haysom da cewa mutum ne da ba a maraba da shi a kasar.
-
Gabon : Ali Bongo Ya Yi Jawabi A Karon Farko Tun Bayan Da Ya Fara Jinya
Jan 01, 2019 14:34A karon farko, tun bayan da ya fara jinya, shugaba Ali Bongo Odimba na Gabon, ya yi jawabi ga al'ummar kasar.
-
Chadi : Za'a Gudanar Da Zabuka A Cikin Watanni Masu Zuwa_Deby
Jan 01, 2019 12:19Shugaban Kasar Chadi Idriss Deby ya ce za'a gudanar da zabubukan kasar da suka hada dana 'yan majalisar dokoki da kuma na kananen hukumomi a tsakiyar wannan sabuwar shekara ta 2019.
-
An Sauke Babban Komandan Sojojin Kasar Zambia Daga Mukaminsa.
Jan 01, 2019 03:21Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu ya bada sanrawan tube babban komandan sojojin kasar Paul Mihova da kuma mataimakinsa Jackson Miti daga mukamansu, sannan ya maye gurbinsu da William Sikazwe.