Moroko: An Rusa Wata Kungiya Mai Fataucin Mutane
'Yan Sandan kasar Moroko sun sanar da rusa wata kungiyar masu fataucin mutane a kusa da birnin Ribat
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato majiyar 'yan sandan na cewa; Mutane biyu da aka kama masu shekaru 35 da 39 suna jigilar 'yan gudun hijira ba bisa ka'ida ba.
Majiyar 'yan sandan ta kara da cewa; An kuma tsaida wasu motoci guda uku mallakin mutanen da aka kama.
A shekarar 2018 da ta gabata, kasar Moroko ta fuskanci karuwar fataucin mutane fiye da shekarun baya
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Moroko ta ce; Daga watan Janairu zuwa Nuwamba a shekarar 2018 da ta shude, an rusa kungiyoyin masu fataucin mutane 174 wanda yake nuna karuwar matsalar idan aka kwatanta da shekarar 2017
Sai dai duk da haka an sami 'yan gudun hijira da su ka ratsa ta kasar Moroko suka kutsa cikin kasar Spain har su 55,000 a cikin shekarar da ta gabata