An Sauke Babban Komandan Sojojin Kasar Zambia Daga Mukaminsa.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34638-an_sauke_babban_komandan_sojojin_kasar_zambia_daga_mukaminsa.
Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu ya bada sanrawan tube babban komandan sojojin kasar Paul Mihova da kuma mataimakinsa Jackson Miti daga mukamansu, sannan ya maye gurbinsu da William Sikazwe.
(last modified 2019-01-01T03:21:54+00:00 )
Jan 01, 2019 03:21 UTC
  • An Sauke Babban Komandan Sojojin Kasar Zambia Daga Mukaminsa.

Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu ya bada sanrawan tube babban komandan sojojin kasar Paul Mihova da kuma mataimakinsa Jackson Miti daga mukamansu, sannan ya maye gurbinsu da William Sikazwe.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya ce shugaba Lungu bai bayyana dalilai na sauke wadanan manya-manyan sojojin kasar daga mukamansu ba, amma a lokacinda yake rantsar da sabon babban komandan sojojin kasar ya bukace ci da ya kula da aikinsa kamar yadda yakamata kada kuma ya yi amfani da matsayinsa inda bai dace ba. 

Shugaba Lungu ya kara da cewa an san sojojin kasar Zambia da halaye mai kyau a ciki da wajen kasar, don haka yana fatan sabbin shuwagabannin sojojin kasar zasu kiyaye wannan matsayin da sojojin kasar suke da shi.

Shugaban kasar Zambia da ya gabata ne Michael Sata ya nada Jackson Miti a matsayin babban komandan sojojin kasar ta Zambia a shekara ta 2011.