Somaliya Ta Kori Wakilin Majalisar Dinkin Duniya
Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Somaliya ta bayyana wakilin majalisar Dinkin Duniya a kasar, Nicholas Haysom da cewa mutum ne da ba a maraba da shi a kasar.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Somaliya ta zargi wakilin na Majalisar Dinkin Duniya da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar.
Shi dai Haysom ya bukaci gwamnatin Somalia da ta yi bayani akan kame Mukhtar Robow wanda tsohon dan kungiyar al-shabab ne amma ya sauya zuwa dan siyasa. Har ila yau wakilin na Majalisar Dinkin Duniya ya yi tir da kisan da aka yi wa magoya bayan Robow a lokacin da su ka gudanar da Zanga-zanga
Antonio Gutrress ne dai ya dana Nicholas Haysom a matsayin wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Somaliya a cikin watan Disamba na shekarar 2018 da ta kare.