Congo: An Dakatar Da Allurar Rigakafin Ibola Saboda Rashin Tsaro
Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta sanar da dakatar da allurar rigakafin saboda rikice-rikicen da su ka kunno kai sanadiyyar zabe
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato majiyar ta ma'aikatar Lafiya na cewa: Wuraren da aka dakatar da yin allurar saboda Zanga-zangar da mutane su ke yi bayan zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa, sun kunshi Goma, Beni Butmebo, sai kuma Komanda da Mabalako.
Daga watan Agusata na 2018 zuwa yanzu an yi wa mutane 54,000 ne kawai allurar ta rigakafi.
Adadin mutane da bullar cutar a bayan nan ya kashe sun kai 363
Jam'iyyun adawa a kasar ta Demokradiyyar Congo sun yi zargin cewa ba a gudanar da zabukan cikin tsari ba
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai aka gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki da kananan hukumomi. Sai dai har zuwa yanzu ba a fara sanar da sakamako ba.
A jiya Talata ma dai mahukunta a kasar ta Demokradiyyar Congo sun katse hanyar sadawar ta Internet.
Tun samun 'yancin wannan kasa daga 'yan mulkin mallakar Belgium ne a 1960 dai ta fada cikin rashin tsaro wanda yake ci gaba har yanzu