Pars Today
Gwamnatocin kasashen Iran da Philipines suna gudanar da ayyukan hadin gwiwa a bangaren samar da abincin halal.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasimi ya bayyana cewa zaman lafiyan da kasashen turai suka samu a halin yanzu donn kokarin da kasar Iran ta yi ne a fagen yaki da ayyukan ta'addanci.
Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta yi allawadai da matakin mahukuntan birnin Londan, na haramtawa da kuma sanya kungiyar Hezbollah, ta kasar Lebanon, cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.
Sakamakon rikicin da ya kunno kai tsakanin kasashen Pakistan da India, kasar Iran na kokarin ganin an yi sulhu a tsakanin kasashen biyu.
Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Yi Fatan Ganin An Kafa Alaka Mai Karfi Da Kasar Armenia.
Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya tattauna da wayar tarho da takwaransa na Pakistan Mahmud Kurashi inda ya bukaci ganin an kai zuciya nesa.
Shugaba Rauhani yaki amincewa da murabus din da ministan harkokin wajen kasar ta Iran Muhammad Jawad zarif ya mika, yana mai cewa wajibi ne na kasa ya rataya kan zarif ya ci gaba da gudanar da aikinsa domin kare diflomasiyyar kasar Iran a duniya.
Shugaba Hassan Rauhani na Iran ya bayyana cewa, da sannu al'ummar kasar Iran za su karya lago dukkanin takunkuman da Amurka ta kakaba wa kasarsu.
Jagoran juyin musulinci na kasar Iran ya bayyana cewa Al'ummar kasar Iran ta kara samun karfi na fiye da shekaru 40 din da suka gabata yayin da makiyanta ke kara raunana
Gwamnatin kasar Iran ta yi kira ga kasashen India da Pakistan su kai zuciya nesa a sabanin da ya shigo tsakaninsu a baya-bayan nan.