Rauhani Yaki Amincewa Da Murabus Din Zarif
(last modified Wed, 27 Feb 2019 18:52:41 GMT )
Feb 27, 2019 18:52 UTC
  • Rauhani Yaki Amincewa Da Murabus Din Zarif

Shugaba Rauhani yaki amincewa da murabus din da ministan harkokin wajen kasar ta Iran Muhammad Jawad zarif ya mika, yana mai cewa wajibi ne na kasa ya rataya kan zarif ya ci gaba da gudanar da aikinsa domin kare diflomasiyyar kasar Iran a duniya.

Rauhani ya bayyana Zarif a matsayin bababn gwarzo wanda ya taka gagarumar rawa a bangarori daban-daban ta fuskar diflomasiyyar kasar Iran, wanda kuma har yanzu kasar na da bukatarsa, akan haka Rauhani ya ce bai amince da wannan murabus ba.

Su ma a nasu bangaren ‘yan majalisar dokokin kasar Iran ba su amince da murabus din Zarif, inda suka rubuta wata wasika da suka sanya ma hannu zuwa ga shugaba Rauhani, suna kiransa da cewa kada ya yarda ya amince da murabus din Zarif, domin kuwa kasar ta Iran tana da matukar bukatarsa a irin wannan lokaci.

Yanzu haka Zarif ya amince da cewa zai ci gaba da aikin nasa a matsayin ministan harkokin wajen Iran.