-
Ayatullah Khamenei Ya Gana Da Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin
Nov 01, 2017 14:48Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar irin nasarorin da ake samu a kasar Siriya a fadar da ake yi da ta'addanci na nuni da cewa Iran da kasar Rasha za su iya aiki tare wajen cimma manufofin da suka yi tarayya kanta yana mai cewa ko shakka babu ana iya mai da Amurka ta zamanto saniyar ware sannan kuma takunkumin da ta sanya wa kasashe su zamanto aikin baban giwa.
-
Jami'an Tsaron Iran Sun Wargaza Wasu Kungiyoyi Masu Fasakwabrin Kwayoyi A Yankin Kirman
Oct 31, 2017 15:19Majiyar ma'aikatar yansandan ciki a nan Iran ta bada labarin cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasara wargaza wasu gungun masu fasa korin miyagun kwayoyi biyu a yankin Kirmon da ke kudancin kasar .
-
Rauhani : Amurka Na Son Sanya Yanke Kauna A Zukatan Iraniyawa
Oct 31, 2017 03:20Shugaban jamhuriyar musulinci ta Iran ya ce Amurkawa na kokarin kulla makirci ne domin sanya kokwanto a cikin zukatan al'ummar kasar Iran game da makomar tattalin arzikin kasarmu da kuma ci gabanta.
-
Ruhani Ya Ki Amincewa Da Bukatar Ganawa Da Trump A MDD
Oct 30, 2017 02:19Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da labarin da ke cewa shugaban kasar Hasan Ruhani ya ki amincewa da bukatar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gabatar masa na yana son su gana da kuma tattaunawa da shi a bayan fagen taron babban zauren MDD karo na 72 da aka gudanar a kwanakin baya.
-
MDD Ta Amince Da Shawarar Iran Kan Kwance Damarar Makaman Nukliya A Duniya
Oct 29, 2017 02:50Duk tare da kokarin gwamnatin Amurka na hana shawarar Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan kwance damarar kasashe wadanda suka mallaki makaman nukliya, MDD ta amince da shawarar a jiya Asabar.
-
Kashani:Babu Batun Tattaunawa Game Da Karfin Tsaron Iran
Oct 27, 2017 15:29Limamin da ya jagoranci sallar juma'a na nan birnin tehran Ayatollah ImaMI Kashani ya bayyana cewa babu batun tattaunawa game da karfin tsaron Iran
-
Iran : Jagora Ya Gana Da Firayi Ministan Iraki
Oct 26, 2017 07:51Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya gana da firayi ministan Iraki, Haidar Al-Abadi yau a birnin Tehran.
-
Ayat. Khamenei: Iran Ba Za Ta Taba Tattaunawa Kan Karfinta Na Soji
Oct 26, 2017 02:18Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Iran ba za ta taba tattaunawa da wani kan karfin da take da shi na kare kanta daga makiya ba, yana mai sake jaddada aniyar kasar Iran na ci gaba da kara irin karfin kariya da take da shi duk kuwa da maganganun da makiya suke yi.
-
Swizland Ta Dauki Alhakin Shiga Tsakanin Iran Da Saudiya Don Biyan Bukatun Kasashen Biyu
Oct 25, 2017 15:32A yau Laraba ce Jami'an ofishin jakadancin Swizland a nan Tehran suka rattaba hannun kan yarjejeniyar bude ofishin kare manufofin kasar Iran a Saudiya amma karkashin ofishin jakadancin Swizland a birnin Riyadh.
-
Wata Kotu A Iran Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Dan Leken Asirin 'Isra'ila' A Kasar
Oct 24, 2017 14:20Babban mai shigar da kara ba birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewar an yanke hukuncin kisa a kan wani mutum da aka same shi da laifin gudanar da ayyukan leken asirin Iran wa haramtacciyar kasar Isra'ila.