Iran : Jagora Ya Gana Da Firayi Ministan Iraki
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya gana da firayi ministan Iraki, Haidar Al-Abadi yau a birnin Tehran.
A jiya ne Al-abadi ya iso nan Tehran bayan ziyara da ya kai a Turkiyya a ci gaba da ran gadin da yake yi a wasu kasashen yankin gabas ta tsakiya.
A yayin ganawar, jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, ya bayyana cewa hadin kan kabilun Iraki da kuma goyan bayan gwamnatin Bagadaza shi ne tushen nasara da kasar ta samu wajen murkushe 'yan ta'adda da masu goyan bayansu a kasar.
Kazalika kuma jagoran, ya goyi bayan gwamnatin Irakin kan kare hadin kan kasar da zamanta dunkulalliya wacce kuma take da babban mahimmanci a kasashen Larabawa.
Jagoran ya kuma shawarci mahukuntan Iraki da su yi taka tsan-tsan akan makircin Amurka.