Rauhani : Amurka Na Son Sanya Yanke Kauna A Zukatan Iraniyawa
(last modified Tue, 31 Oct 2017 06:50:23 GMT )
Oct 31, 2017 06:50 UTC
  • Rauhani : Amurka Na Son Sanya Yanke Kauna A Zukatan Iraniyawa

Shugaban jamhuriyar musulinci ta Iran ya ce Amurkawa na kokarin kulla makirci ne domin sanya kokwanto a cikin zukatan al'ummar kasar Iran game da makomar tattalin arzikin kasarmu da kuma ci gabanta.

A karshen wani taron hadin gwiwa tsakanin shugaban kasar Iran, Shugaban majalisar shawarar musulinci  da shugaban ma'aikatar shara'ar kasar da ya gudana a daren jiya litinin, Shugaban jamhuriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan rauhani ya jadadda godiyarsa ga al'umma da kuma mahukuntan kasar saboda kiyaye hadin kan da suke da shi, inda ya ce hakan ya ruguza duk wani kokarin makiya da masu girman kai na samar da rashin tsaro,da fadada 'yan ta'adda a yankin.

A yayin da yake ishara kan kokarin girman kai na canza iyakokin kasashen yankin, shugaba Rauhani ya ce makarkashiya da makircin da masu girman kan ke yi bai iya cin nasara ba, kuma a halin da ake ciki, yankin na halin fice wannan shiri.

Yayin da yake ishara kan kokarin makiya na sanya sabani a yankin domin sayar da makamansu, Shugaba Rauhani ya ce domin magance sabanin dake akwai a yankin, kamata yayi mu fadada aiki tare da kume lalubo hanyar magance shi.

A daren jiya Litinin ne, Shugaban majalisar musulinci na kasar Dakta Ali Larijani ya karbi bakuncin shugaban jumhoriyar musulinci ta Iran dakta Hasan Rauhani, da shugaban ma'aikatar shara'ar kasar Ayatollahi Sadik Amuly Larijani a majalisar inda suka tattauna kan mahiman batutuwan da suka shafi kasar da yankin.