-
Italiya Za Ta Kwashe Wani Adadi Na Sojojinta Daga Iraki Ta Mayar Da Su Nijar
Dec 25, 2017 08:52Firaministan kasar Italiya ya gabatar da wani shiri na kwashe wani adadi na sojojin kasar sa daga kasar Iraki, domin tura su jamhuriyar Nijar domin ayyukan yaki da ta'addanci da kuma masu safarar miyagun kwayoyi a cikin watanni masu zuwa.
-
Guatemala Ta Bayyana Shirinta Na Bin Sahun Kasar Amurka Na Maida Ofishin Jakadancinta Zuwa Qudus
Dec 25, 2017 03:17Shugaban kasar Guatemala ya sanar da shirin gwamnatinsa na bin sahun kasar Amurka na maida ofishin jakadancin kasarsa da ke birnin Tel-Aviv na haramtacciyar kasar Isra'ila zuwa birnin Qudus.
-
Tsayin Dakan Kasashen Afirka Wajen Tinkarar Barazanar Trump Kan Qudus
Dec 25, 2017 01:47A daidai lokacin da gwamnatin Amurka take ci gaba da barazana ga kasashen duniya dangane da batun Kudus, kasashen Afirka suna daga cikin kasashen duniya da suka tsaya kyam wajen goyon bayan al'ummar Palastinu da kuma yin watsi da matsayar shugaban Amurkan kan birnin Kudus.
-
Boswana Ta Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka
Dec 24, 2017 02:56Gwamnatin kasar Boswana ta maida martani mai zafi ga barazanar Amurka kan goyon bayan da ta bawa kudurin yin Allah wadai da matsayin shugaban kasar Amurka dangane da birnin Quds.
-
Kimanin Rabin Mutanen Amurka Basa Goyon Bayan Trump Kan Matsayinsa Dangane Da Birnin Qudus
Dec 24, 2017 02:56A wani jin ra'ayin da tashar talabijin ta CNN ta gudanar kusan rabin mutanen kasar Amurka basa goyon bayan shugaban kasar kan matsayin da ya dauka na goyon bayan HKI dangane da Qudus.
-
Yan Majalisar Dokoki Amurka 24 Sun Bukaci Gwamnatin Trump Ta Dauki Matsayi Kan Iran
Dec 24, 2017 02:55Wakilan majalisar dokokin kasar Amurka 24 yan jam'iyyar Republican sun rubuta wasika zuwa gwamnatin shugaba Donald Trump kan abin da suka kira sabuwar yarjejeniyar Nukliyan da kasar Iran ta yi.
-
MDD Ta Fara Kwashe Bakin Haure Daga Libya Zuwa Italiya
Dec 23, 2017 07:50Babban kwamishinan dake kula da 'yan gudun hijra na MDD ya sanar da fara kwashe bakin haure daga kasar Libiya zuwa kasar Italiya
-
An Nada Shugabar Asusun Kula Da Kananen Yara Na MDD UNICEF
Dec 23, 2017 07:49An nada Henrietta Fore 'yar kasar Amurka shugaban Asusun kula da kananen yara na Majalisar Dinkin Duniya.
-
Commonwealth Ta Yi Kiran A Magance Rikicin Da Ya Kunno Kai A Kamaru Cikin Ruwan Sanyi
Dec 23, 2017 01:53Babbar sakatariyar kungiyar kasashen renon Ingila (Commonwealth), Patricia Scotland, ta kirayi gwamnatin kasar Kamaru da ta dau matakan ruwan sanyi da kuma tattaunawa wajen magance rikicin da ya kunno kai a yankunan da suke magana da harshen Turancin Ingila na kasar.
-
Kwamitin Tsaro Ya Sake Sanya Wa Koriya Ta Arewa Takunkumi Saboda Gwajin Makamai Masu Linzami
Dec 23, 2017 01:52Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya sake sanya wa kasar Koriya ta Arewa wani sabon takunkumi sakamakon sake gwajin makamai masu linzami masu cin dogon zango da kasar ta yi.