Boswana Ta Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka
Gwamnatin kasar Boswana ta maida martani mai zafi ga barazanar Amurka kan goyon bayan da ta bawa kudurin yin Allah wadai da matsayin shugaban kasar Amurka dangane da birnin Quds.
Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto wani bayanin wanda ya fito daga ofishin jakadancin kasar Boswana a MDD yana maida martani ga wasikar Nicky Haley jakadiyar Amurka a MDD kan goyon bayan da Boswana ta bawa Palasdinawa a zaben ranar Alhamis.
Kafin haka dai Nicky Haley ta yi barazana yanke tallafin da Amurka take bawa duk wata kasa wacce ta ki goyon bayan Amurka dangane da matsayinta kan birnin Qudus.
Bayanin ya kara da cewa barazanar Nicky Haley ga kasar Boswana yana dai-dai da kwace 'yancin da kasar take da shi ne.
Kasar Boswana dai tana daga cikin kananan kasashe Afrika wadanda basa da karfin tattalin arziki, kuma mafi yawan abin da suke samu na fitowa ne daga tallafin da Amurka da sauran manyan kasashen duniya suke bayarwa.
A kuri'ar da aka kada babban zauren MDD a ranar Alhamis kasashe 128 ne suka ki amincewa da matsayin Amurka dangane da Birnin Qudus sannan kasashe 9 kacal suka goyi bayanta. Wannan ya nuna mafi yawan kasashen duniya basa tare da Amurka a wannan fagen.