MDD Ta Fara Kwashe Bakin Haure Daga Libya Zuwa Italiya
Babban kwamishinan dake kula da 'yan gudun hijra na MDD ya sanar da fara kwashe bakin haure daga kasar Libiya zuwa kasar Italiya
Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya habarta cewa wani jirgin sojin Italiya ya fara kwashe tawagar farko na 'yan gudun hijra da suka hada da Mata da kananen yara a jiya juma'a daga sansanin da ake tsare da su a Libiya zuwa kasar Italiya.
Jirgin farko na sojojin Italiya kirar C-130 ya sauka ne a kasar dauke da mata 110, da kuma kananan yara, yayin da jirgi na biyu ke dauke da wasu bakin hauren sama da 50.
Dubban bakin-haure ne ke makale a Libya, inda ake tsare da su, a sansanonin kasar tamkar bayi, tare da gana musu azaba, bayan yunkurin da suka yi na ketarwa zuwa nahiyar turai.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta yi hasashen cewa, akalla bakin-haure dubu 18,000 ake ci gaba da tsarewa a sansanoni daban daban a Libya, kuma nan da shekara mai kamawa, tana sa ran kwashe bakin-hauren akalla 10,000 daga kasar.