An Nada Shugabar Asusun Kula Da Kananen Yara Na MDD UNICEF
https://parstoday.ir/ha/news/world-i26631-an_nada_shugabar_asusun_kula_da_kananen_yara_na_mdd_unicef
An nada Henrietta Fore 'yar kasar Amurka shugaban Asusun kula da kananen yara na Majalisar Dinkin Duniya.
(last modified 2018-08-22T11:31:11+00:00 )
Dec 23, 2017 11:19 UTC
  • An Nada Shugabar Asusun Kula Da Kananen Yara Na MDD UNICEF

An nada Henrietta Fore 'yar kasar Amurka shugaban Asusun kula da kananen yara na Majalisar Dinkin Duniya.

A daren jiya juma'a ne aka zabi Henrietta Fore mai shekaru 69 da haihuwa 'yar  kasar Amurka a matsayin sabuwar shugabar  Asusun kula da kananen yara na MDD wacce ta maye gurbin Anthony Lake da ya jagorancin asusun tun daga shekarar 2010.

Mai magana da yawun sakatare janar na MDD ya bayyana cewa  shekaru 40 da suka gabata zuwa yanzu  Henrietta Fore ta kasance cikin hidima ga al'ummar Amurka da kuma wasu cibiyoyin fararen hula na kasar.

Babban sakatare janar na majalisar dinkin duniya ya yi ishara da cewa kashi hudu cikin dari na wannan hukuma na a hanun mata ne, domin haka wannan nadi zai kara bawa matan karfin gwiwa wajen ci gaba da ayyukansu kamar yadda ya kamata.