-
Shugabannin Rasha da Faransa Sun Tabbatar Da Ci Gaba Da Girmama Yarjejeniyar Nukiliyar Iran
Nov 03, 2017 02:23Shugabannin kasashen Rasha, Vladimir Putin da Faransa Emmanuel Macron sun sake tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da kasar Iran bugu da kari kan wajibcin ci gaba da aiwatar da ita.
-
Yau Ne Duniya Ke Tuni Da Ranar Yaki Da Cin Zarafin ‘Yan Jaridu
Nov 02, 2017 14:47Yau ne ake bikin ranar yaki da yadda ake cin zarafin ‘yan Jaridu ta duniya, ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin fadakar da mutane muhimmancin aikin Jaridu da kuma basu kariyar da ta dace.
-
Kungiyar Kare Hakkin Bil-Adama Ta Amnesty International Ta Yi Suka Kan Kasar Aljeriya
Nov 02, 2017 02:48Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan gwamnatin Aljeriya dangane da yadda take gudanar da mummunar mu'amala ga bakin haure musamman fitar da su daga cikin kasarta ta hanyar musgunawa.
-
Ministan Harkokin Wajen Faransa Zai Ziyarci Iran
Nov 01, 2017 02:13Ministan harkokin wajen kasar Faransa, Jean-Yves Le Drian, ya bayyana zai ziyarci kasar Iran a cikin kwanaki masu zuwa domin share fagen ziyara da shugaba Emanuelle Macron zai kawo a nan Tehran.
-
Kwamitin Tsaro Na MDD Ya Bukaci A Kare Yara A Lokutan Yaki
Nov 01, 2017 02:11Kwamitin sulhu na MDD ya bukaci dukkan bangarorin dake da hannu a duk wani rikici dasu kare yara a wuraren da ake yake-yake tare da neman kare hakkokinsu a irin wannan yanayi.
-
Amurka : Mutum 8 Suka Hallaka A Harin Manhattan
Nov 01, 2017 02:10Hukumomi a birnin New York na Amurka sun ce mutum takwas suka mutu kana wasu 11 suka raunana biyo bayan da wani mahari a cikin wata mota ya aukawa matafiya akan wata hanyar 'yan kekuna dake a yankin Manhattan.
-
Shugaban Majalisar Zartarwa A Afganistan Ya Bukaci Ficewar Sojojin Kasashen Waje Daga Kasar
Oct 31, 2017 15:22Shugaban majalisar zartarwa ta kasar Afganistan Abdallah Abdallah ya bukaci sojojin kasashen waje su bar kasar Afganistan, don mutanen kasar ba sa kaunar zamansu a cikin kasar.
-
Amurka Ta Gargadi 'Yan Kasarta kan Nisantar Gudanar Da Tafiye-Tafiye Zuwa Kasar Niger
Oct 31, 2017 08:36Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta gargadi Amurkawa da su guji gudanar da tafiye-tafiye zuwa Jamhuriyar Niger sakamakon barazanar ayyukan ta'addanci a kasar.
-
Shugaban Yankin Catalonia Yayi Hijra Zuwa Birnin Brussels
Oct 31, 2017 03:17Tsohon shugaban yankin catalonia na kasar Spaniya tare da wasu manbobin tsohuwar gwamnatin biyar sun gudu zuwa birnin Brussels na kasar Belgium.
-
Rasha : Putin Zai Ziyarci Iran Ranar Laraba
Oct 30, 2017 13:35Fadar Shugaban kasar Rasha ta Kremlin ta sanar da cewa shugaban kasar Vladimir Putin zai kai wata ziyara a birnin Tehran na jamhuriya musulinci ta Iran.