Amurka : Mutum 8 Suka Hallaka A Harin Manhattan
Hukumomi a birnin New York na Amurka sun ce mutum takwas suka mutu kana wasu 11 suka raunana biyo bayan da wani mahari a cikin wata mota ya aukawa matafiya akan wata hanyar 'yan kekuna dake a yankin Manhattan.
Harin wanda hukumomin suka danganta dana ta'addanci, shi ne irinsa na farko da ya hallaka mutane tun bayan na 11 ga watan Satumba 2001 a birnin New York.
Magajin garin Birnin New York Bill de Blasio, ya ce bisa ga bayyanan farko-farko da aka samu harin na da nasaba da na ta'addanci.
A wani taron manema labarai, kwamishinan 'yan sandan birnin James O' Neil, ya ce wanda ake zargi da kai harin mai shekaru 29 ba dan birnin na New York ba ne.
A wani sako a shafinsa na twitter, shugaba Donald Trump ya danganta mutumin da mai tabin hankali, tare da cewa jami'an tsaro na bibiyar batun sau da kafa, tare da shan alwashin kawo karshen hakan a wannan kasa ta AMurka.