Ministan Harkokin Wajen Faransa Zai Ziyarci Iran
Ministan harkokin wajen kasar Faransa, Jean-Yves Le Drian, ya bayyana zai ziyarci kasar Iran a cikin kwanaki masu zuwa domin share fagen ziyara da shugaba Emanuelle Macron zai kawo a nan Tehran.
Ko da yake Mista Le Drian bai bayyana takamaimai ranar da kai ziyara ba, aman ya ce tana da manufar tattaunawa akan yarjejeniyar nukiliyar da mayan kasashen duniya suka cimmawa da Iran bayan da shugaba Donald Trum na Amurka ya ki amunce sanyawa yarjejeniyar hannu.
Faransa ta bakin ministan harkokin wajenta ta jaddada adawa da duk wani yunkuri na canza abunda yarjejeniyar ta kunsa.
Ministan ya ce ba'a dai fidda rana da shugaba Emanuelle zai ziyarci Teheran ba.
Idan har ziyara ta tabbata ita ce irinta ta farko da wani shugaban faransa zai kawo Iran tun bayan shekara 1976.