Rasha : Putin Zai Ziyarci Iran Ranar Laraba
Fadar Shugaban kasar Rasha ta Kremlin ta sanar da cewa shugaban kasar Vladimir Putin zai kai wata ziyara a birnin Tehran na jamhuriya musulinci ta Iran.
Mista Putin zai tattauna da takwaransa na Iran din Dakta Hassan Ruhani da kuma na Azerbaijan Ilham Aliev kamar yadda fadar ta Kremlin ta sanar a yau.
Shuwagabannin guda uku zasu maida hankali kan batutuwan da suka shafi kasashen da siyasa da tattalin arziki al'adu da kuma jin kai.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da shuwagabbanin kasashen na Iran da Rahsa da Azerbaijan suka hadu a teburin tattaunawa ba, don ko a bara sun yi irin wannan ganawa a Baku babban birnin kasar Azerbaijan.
Da yake karin haske kan ziyarar da shuwagabannin biyu zasu kawo a nan Tehran, karamin ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Ebrahim Rahimpur, ya ce bangarorin uku kuma zasu tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliyar da Iran ta cimmawa da mayan kasashen duniya musamen kan kace nace da akeyi a kanta bayan da shugaban Amurka Donald de Trump ya amunce sanya mata hannu.