-
G20 / Afirka : Merkel Za Ta Gana Da Wasu Shugabannin Afrika
Jun 12, 2017 01:14Kasar Jamus wacce ke rikeda shugabannin kungiyar kasashe mafi arziki a duniya na G20 na son karfafa alakar kasuwanci ta hanyar zuba jari a nahiyar Afrika a wani mataki na yaki da kwararar bakin haure.
-
Faransa : Jam'iyyar Shugaba Macron Na Kan Gaba A Zaben Majalisar Dokoki
Jun 12, 2017 01:14Rahotanni daga Faransa na cewa jam'iyyar shugaba Emanuelle Macron da jami'yyar MoDem dake kawance da ita na kan gaba da rinjaye a zaben yan majalisar dokokin kasar zagaye na farko da aka kada kuri'arsa a jiya Lahadi.
-
Majami’a Na Bayar Da Abincin Buda Baki A Australia
Jun 11, 2017 17:07Majami’ar birnin Perth na kasar Australia na bayar da buda baki a cikin watan Ramadan mai alfarma.
-
An Fara Zaben 'Yan Majalisa A Faransa
Jun 11, 2017 07:43Al'ummar Kasar Faransa na kada kuru'unsu domin zaben sabbin wakilan majalisar kasar karkashin sabon Shugaban kasa Emmanuel Macron
-
Dakarun Iraki Sun Kwato Yankin "Al-Zanjili" Daga Hannun 'Yan Ta'addan Da'esh
Jun 10, 2017 12:40Rundunar sojin kasar Iraki ta ba da sanarwar cewa dakarun kasar sun sami nasarar kwato yankin Al-Zanjili da ke yammacin garin Mosul daga hannun 'yan ta'addan Da'esh (ISIS) lamarin da ke nuni da cewa sauran 'yan wasu yankuna ne kawai suka rage a hannun 'yan ta'adda.
-
Ethiopia da Masar Sun Bukaci MDD Da Ta Dakatar Da Sammaci Kama Al-Bashir
Jun 10, 2017 12:40Kasashen Ethiopia da Masar sun bukaci Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya dakatar da binciken da kuma shari'ar da Kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffuka (ICC) ta ke yi wa shugaban kasar Sudan Umar Hasan al-Bashir.
-
Theresa ta Nemi Gafarar Wakilan Jam'iyarta A Majalisa
Jun 10, 2017 07:23Firaministar Birtaniya Theresa May ta nemi gafarar wakilan Jam'iyarta dake Majalisar dokokin kasar biyo bayan shan kayin da jam'iyar su ta yi a zaben 'yan Majalisun da aka gudanar
-
Amurka : Trump Ya Zargi Comey Da Yi Masa Karya
Jun 10, 2017 01:21Shugaba Donald Trump na Amurka ya zargi koraren shugaban hukumar bincike ta FBI, James Comey da yi masa karya.
-
Birtaniya: Jam'iyyar Conservative Ba Ta Samu Rinjayen Da Take Bukata Ba
Jun 09, 2017 01:56Rahotanni daga Burtaniya na nuni da cewa sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin da aka gudanar jiya, jam'iyyar masu ra'ayin rikau mai mulki ba ta samu rinjayen da take bukata ba.
-
Tsohon Shugaban FBI: Donald Trump Makaryaci Ne
Jun 09, 2017 01:55Tsohon shugaban hukumar tsaro ta FBI a Amurka ya bayyana shugaban kasar Amurka Donald Trump da cewa mutum ne makaryaci.