Amurka : Trump Ya Zargi Comey Da Yi Masa Karya
Shugaba Donald Trump na Amurka ya zargi koraren shugaban hukumar bincike ta FBI, James Comey da yi masa karya.
Mista Trump ya ce a shirye yake ya yi bayyani dala-dala bisa rantsuwa kan karya da Comey ya yi masa kan cewa ya bukace da a dakatar da bincike kan tsohon mashawarcinsa kan harkar tsaro Michael Flynn.
A ranar Alhamis data gabata ce Mista Comey wanda ya gurfana gaban kwamitin Majalisar Dattijan Amurka ya ce Trump ya bukaci ya ma sa biyayya tare da dakatar da binciken tsohon mai ba shi shawara kan sha’anin tsaro Mike Flynn kan zargin kutsen da akewa Rasha a zaben shugaban kasar.
Shi dai Mista Trump ya ce lalle akwai abubuwa da dama da suka tattauna wanda Comey ya bayyana, saidai ya zuzuta wasu bayannan.
Mista Comey wanda Trump ya tube a ranar 9 ga Mayu ya ce an tube shi ne don sauya akalar binciken Rasha.