Majami’a Na Bayar Da Abincin Buda Baki A Australia
https://parstoday.ir/ha/news/world-i21230-majami’a_na_bayar_da_abincin_buda_baki_a_australia
Majami’ar birnin Perth na kasar Australia na bayar da buda baki a cikin watan Ramadan mai alfarma.
(last modified 2018-08-22T11:30:14+00:00 )
Jun 11, 2017 21:37 UTC
  • Majami’a Na Bayar Da Abincin Buda Baki A Australia

Majami’ar birnin Perth na kasar Australia na bayar da buda baki a cikin watan Ramadan mai alfarma.

Shafin yada labarai na IBC ya bayar da rahoton cewa, a karon farko majami’ar birnin Perth na Australia ta kirayi buda baki da ya hada musulmi da kiristoci a wuri guda.

Faidil shi ne limamin musulmi a birnin na Perth ya bayyana cewa, tsawon shekaru shida kenan a jere a kowane watan Ramadan majami’ar birnin tana shirya wa musulmi buda baki, amma a wannan shekara ta shirya buda bakin ne tare da gayyatar musulmi da kiristoci.

Malamin ya ce hakika wannan lamari ne da ke cike da hikima, domin kuwa a wannan lokacin kiyayya da musulmi na kara kamari a tsakanin al’ummomin kasar ta Australia wadanda mafi yawa kiristoci ne, amma shirya irin wannan buda baki zai sanya kiristoci da dama su fahimci yadda musulmi suke da halayensu, sabanin yadda suke tunani.