-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tofin Allah Tsine Kan Kisar Fararen Hula A Kasar DR Congo
May 07, 2017 00:58Ofishin kula da jin kan bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya {OCHA} a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ya yi tofin Allah tsine kan abin da ya kira kisan kiyashi kan fararen hula a lardin Kasai da ke tsakiyar kasar DR Congo.
-
Zaben Shugaban Kasar Faransa Zagaye Na Biyu
May 07, 2017 00:55Yau Lahadi 7 ga watan Mayu Al'ummar kasar Faransa ke kada kuri'un su cikin kwararen matakan tsaro domin zaben Sabon Shugaban da zai karbi hayar fadar Elysee a tsakanin Marine Le Pen da Emmanuel Marcon.
-
Zaben Faransa : Ba Zamuyi Kyaliya Kan Kutse Ba, Hollande
May 06, 2017 12:26Shugaban kasar Faransa mai barin gado, Faransoi Hollande ya bayyana cewa kutse da akayi dan takara a zaben shugabancin kasar Emanuelle Macron ba zai taba kasancewa ba abun kyaliya.
-
Iran Ta Kai Kukan Saudiyya MDD Saboda Hada Baki Da 'Yan Ta'adda Da Ke Barazana Ga Tsaron Kasar
May 05, 2017 05:17Jakadan Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Gholamali Khoshroo ya bayyana cewar maganganun baya-bayan nan na ministan tsaron Saudiyya kuma mataimakin yarima mai jiran gadon kasar Yarima Muhammad bn Salman kan Iran wata barazana ce a fili ga tsaron kasar Iran kana kuma wani nau'i ne na yarda da hadin gwuiwan dake tsakanin gwamnatin Saudiyya da ayyukan ta'addancin da kungiyoyin 'yan ta'adda suke yi a Iran.
-
Mogherini: Ya Kamata A Yi Bincike Kan Kisan Musulmi A Myanmar
May 04, 2017 12:19Gwamnatin kasar Myanmar ba ta amince da gudanar da bincike a kan zargin kisan musulmi a kasar ba.
-
An Bude Babban Baje Kolin Tufafin Mata Musulmi A Indonesia
May 04, 2017 12:19A yau ne aka bude babban baje kolin tufafin mata na musulunci a kasar Indonesia tare da halartar kamfanoni na kasashen ketare.
-
Koriya Ta Arewa Ta Ja Kunnen Japan Cewa Zata Fara Fuskantar Harin Nukiliya Idan Yaki Ya Barke
May 04, 2017 06:53Koriya ta Arewa ta ja kunnen kasar Japan da cewa ita ce kasar farko da za ta fara fuskantar hari da makaman nukiliya matukar dai ya ki ya barke a yankin na su.
-
Faransa : Le Pen Da Macron Sun Tafka Zazzafar Muhawara
May 04, 2017 01:19'Yan takara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Faransa, sun tafka zazzafar muhawarar talabijin a yayin da ya rage kasa da kwanaki hudu a je babban zaben.
-
Shugabannin Kasashen Rasha Da Turkiyya Sun Gana A Tsibirin Sochi Na Kasar Rasha
May 03, 2017 11:52Shugabannin kasashen Rasha da na Turkiyya sun gana a tsibirin Sochi na kasar Rasha, inda suka tattauna harkokin da suka shafi kasashensu da ma duniya baki daya.
-
Wani Hari Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 8 A Birnin Kabul Na Afghanistan
May 03, 2017 06:46Rahotanni daga kasar Afghanistan na nuni da cewa a wani hari wanda daga dukkanin alamu an kai shi ne kan dakarun kungiyar NATO a kusa da ofishin jakadancin Amurka a birnin Kabul, babban birnin kasar Afghanistan din, mutane 8 sun mutu kana wasu sama da 25 kuma sun sami raunuka cikinsu kuwa har da wasu sojojin Amurka su uku.