Faransa : Le Pen Da Macron Sun Tafka Zazzafar Muhawara
-
A ranar 7 ga watan Mayu ne za\'a je zaben shugaban faransa a zagaye na biyu
'Yan takara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Faransa, sun tafka zazzafar muhawarar talabijin a yayin da ya rage kasa da kwanaki hudu a je babban zaben.
Ko wanne daga cikin 'yan takarar biyu, Emmanuel Macron da Marine Le Pen sun kare manufofinsu a zaben, kan batutuwan da suka shafi aiki, tsarona cikin gida, yaki da ta'addanci da kuma makomar kasar a nahiyar turai.
Da yake bayyani kan batun da ya shafi yaki da ta'addanci dan takara mai sassaucin ra'ayi Emanuel Macron ya zargi abokiyar hamayarsa mai tsananin ra'ayin rikau da haddasa yakin basasa a kasar, kafin daga bisani ya ce 'yan ta'adda ne fatan nasararta a zaben.
Saidai da take maida masa martani da zafi Mme Le pen ta ce a cikin duk manufofinsa babu batun yaki da ta'addanci.
Amman daga baya ya fayyace mata manufofin nasa na yaki da ta'addanci wanda ya ce sun dogara akan tattara bayanai da kuma hadin gwiwa kasashen turai.