Zaben Faransa : Ba Zamuyi Kyaliya Kan Kutse Ba, Hollande
Shugaban kasar Faransa mai barin gado, Faransoi Hollande ya bayyana cewa kutse da akayi dan takara a zaben shugabancin kasar Emanuelle Macron ba zai taba kasancewa ba abun kyaliya.
Mista Hollande wanda ke bayyana hakan a yayin da ya ziyarci wani gidan ajiye kayan tarihi na birnin Paris tare da sarkin Marocco, ya ce gagarimin kutsen da akayiwa Macron ba abunda za'a rufe ido a kai ba ne, kuma dama mun san akwai hadarin hakan ta faru a yayin yakin neman zabe, don saboda hakan ta faru a wani waje, saidai ba tare da yin karin haske ba.
Holande ya ce idan hakan ta kasance an dau bayanai cikin imel din dan takara to za'a gudanar da bincike.
A jiya ne tawagar yakin neman zaben dan takara shugaban kasa Faransa dake kan gaba-gaba Emanuelle Macron ta sanar da yi masa gagarimin kuste bayan fallasa wasu dubban takardu a intarnet.
A gobe Lahadi ne ake kada kuri'a a zaben shugaban kasar ta faransa zagaye na biyu inda za'a fafata tsakanin 'yar takara (Front National) mai sananin ra'ayin rikau Marine le Pen da kuma Emanuelle Macron mai sassaucin ra'ayi, wanda hasashen ke nuna cewa zai iya lashe zaben da kashi 61 zuwa 63%.