Zaben Shugaban Kasar Faransa Zagaye Na Biyu
Yau Lahadi 7 ga watan Mayu Al'ummar kasar Faransa ke kada kuri'un su cikin kwararen matakan tsaro domin zaben Sabon Shugaban da zai karbi hayar fadar Elysee a tsakanin Marine Le Pen da Emmanuel Marcon.
Zaben kasar Faransar dai ya zo tungar karshe, inda zuwa karshen sa'o'in wannan rana ta Lahadi zai bayyana wane ne zai shiga fadar Shugaban kasar Faransa dake tattare da matsaloli da dama kama daga matsalar tattalin arziki, zamantakewa, zuwa na Siyasa tsakanin 'yan takara Uwargida Marine Le Pen ta jam’iyyar Front National da Emmanuel Macron mai zaman kansa.
Zaben na Yau na da mahimanci gaske ga kasar Faransa da ma kungiyar kasashen Turai, domin haka ne ma, batun zaben ya mamaye dukkanin wureren zaman 'yan siyasa da Jaridun kasashen Turai,yan takarar biyu na Faransa ko wannansu nada tsarin tattalin arziki, Siyasa, zamantakewa da suka babbanta da juna domin kawo canji da kuma kalubantar matsalar da Al'ummar kasar ke fuskanta, wannan dai shi ne karon farko a jumhoriyar ta biyar na kasar Faransa da 'yan takarar da ba su fito daga manyan jam'iyun kasar ba za su fafata a zagaye na biyu.Mista Emmanuel Macron ya tsaya takara ne ba kalkashin ko wata jam'iya ba, ita kuma Uwar gida Marine Le Pen ta tsaya takarar ne kalkashin jam’iyyar Front National mai akidar tsattsauran ra'ayi. Mista Macron mai ra'ayin zama a cikin kungiyar turai na kare manufofin na zaman kasar cikin kasashen kungiyar Kasashen Turai, bayan zagayen farko na zabe, ya ce idan ba a kawo sauyi a siyasar kungiyar kasashen Turai ba, to ba a za iya cimma manufofin gida kungiyar ba, ita kuma Marine Le Pen dake da kasa da rabin ra'ayin Al'ummar kasar ta na da matsanancin ra'ayin rikau da kuma adawa da 'yan gudun hijira, da baki ga kuma nuna kyama ga wasu al’addu na musulunci da ta ce, sun yi hannun riga da al’addun Faransawa. na neman kuru'unta ta hanyar wannan ra'ayi musaman ga masu irin nata ra'ayin a kasar.
Abinda ya sanya zaben kasar Faransa ya fi daukan hankali, nasarar da 'yar takarar Front National mai akidar tsattauran ra'ayi Marine Le Pen ta samu zuwa tsageye na biyu, a shekarar 2002, Dan takarar Jam'iyar Front National Jean Marine Le Pen ya samu nasarar tsallakawa zuwa zagaye na biyu, inda suka kara da Jacques Chirac, a wancan lokaci, canjin da aka samu ya girgiza siyasar kasar Faransa da kuma ta kasashen Turai, inda dukkanin manyan jam'iyun siyasar kasar suka goyin bayan Jacques Chirac, lamarin da ya sanya ya lashe zaben da kashi 82%, saidai zaben na 2017 ya kawar da mafarkin Jam'iya mai milki wajen ci gaba da jan ragamar kasar, a wannan karo ma mafi yawan 'yan takarar shugabancin kasar ta Faransa sun kwarewa Uwar gida Marine Le Pen baya, tare nuna goyon bayan su ga Dan takara mai zaman kansa Emmanuel Macron, domin haka ma masu sharhi kan harakokin siyasar kasar ta Faransa na ganin cewa Mista Macron ne zai lashe zaben kamar yadda gididdigar jin r'ayin Al'umma kafin zaben ya bayar inda ya kashi 63% yayin da abokiyar hamayarsa ta samu kashi 38%.saidai kuma wani abu dake tayar da hankali ga masu goyon bayan Emmanuel Macron shi ne kwanaki biyu kafin gudanar da zaben, kutsan da ake yi wajen fallasa bayyanan sirri na Dan takarar musaman ma game da kudadensa da ya ajiye a bankunan dake kasashen waje.