Mogherini: Ya Kamata A Yi Bincike Kan Kisan Musulmi A Myanmar
(last modified Thu, 04 May 2017 16:49:58 GMT )
May 04, 2017 16:49 UTC
  • Mogherini: Ya Kamata A Yi Bincike Kan Kisan Musulmi A Myanmar

Gwamnatin kasar Myanmar ba ta amince da gudanar da bincike a kan zargin kisan musulmi a kasar ba.

Shafin yada labarai na asianews.network ya habarta  cewa, Federica Mogherini babbar jami’a mai kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar trai ta bayyana cewa, gudanar da bincike kan zargin kisan musulmi ‘yan kabilar Rohingya a Myanmar zai taimaka matuka wajen gano hakikanin abin da yake faruwa.

Mogherini ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da ministan harkokin wajen kasar Myanmar Ang San Suchi, inda ta ce bisa la’akari da kudirin da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya fitar kana bin da yake faruwa a Myanmar, gudanar da sahihin bincike ne zai iya bayar da damar tantance hakikanin abin da yake faruwa.

Sai dai a nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar ta Myanmar ya bayyana cewa, ba su gamsu da rahoton da kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya suke bayarwa kan rikicin kasar ta Myanmar ba, wanda kuma a kan haka ne kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar duniya ya fitar da kudirinsa.