-
Kudirin Amurka Na Yin Allawadai Da Hamas Ya Ki Karbuwa A MDD
Dec 07, 2018 04:15Kudirin da Amurka ta gabatar na bukatar yin allawadai da kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas, ya kasa samun karbuwa a majalisar dinkin duniya.
-
Zarif: Ko Shakka Babu Iran Za Ta Mayar Da Martani Ga 'Yan Ta'adda Da Masu Goyon Bayansu
Dec 06, 2018 15:49Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar ko shakka babu Iran za ta mayar da martani mai kauci ga 'yan ta'adda da masu goya musu bayan da suka kai harin garin Chabahar da ke Kudu maso gabashin kasar ta Iran yana mai dora alhakin harin a kan 'yan ta'addan da suke samun goyon bayan kasashen waje.
-
MDD: Adadin Mutanen Yemen Da Suke Fuskantar Bala'in Yunwa Na Iya Kai Wa Miliyan 20
Dec 06, 2018 15:49Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar matukar dai ba a isa ga agajin abinci na gaggawa zuwa kasar Yemen ba, to kuwa adadin mutanen da suke fuskantar bala'in yunwa a kasar zai iya kai mutane miliyan 20 daga miliyan 15 din da ake da shi a halin yanzu.
-
EU ta zargi kasashen Afrika da karkatar da kudaden tallafi
Dec 06, 2018 10:37Kungiyar tarayya Turai ta EU, ta zargi kasashen Afrika da karkakar da kudaden tallafi da take basu domin inganta rayuwar al'ummunsu.
-
Tattaunawa Neman Zaman Lafiya A Yemen
Dec 06, 2018 09:59A wani lokaci yau Alhamis ne ake fara wata tattaunawa a Sweden, domin lalubo hanyoyin kawo karshen rikicin kasar Yemen, wanda ya hadassa mutuwar mutane akalla 10,000 a cikin shekara hudu.
-
Tawagar MDD Na Neman Sojojinta 2 A Congo
Dec 06, 2018 09:41Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriya Demuradiyar Congo, ta ce tana neman wasu sojojinta biyu da suka bata tun a watan Nuwamba a yayin wani fada a jihar Beni dake gabashin kasar.
-
Turkiyya Ta Ba Da Umurnin Kamo Jami'an Saudiyya Da Ake Zargi Da Kashe Khashoggi
Dec 05, 2018 16:47Babban mai shigar da kara na garin Istanbul na kasar Turkiyya ya fitar da sammacin kama wasu manyan jami'an kasar Saudiyya kuma na hannun daman Yarima mai jiran gadon kasar su biyu saboda zargin da ake musu na hannu cikin kisan gillan da aka yi wa Jamal Khashoggi.
-
Hizbullah Ta Ja Kunnen 'Isra'ila' Kan Kawo Hari Kasar Labanon
Dec 05, 2018 16:47Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta ja kunnen haramtacciyar kasar Isra'ila da cewa duk wani wuce gona da iri da za ta yi kan kasar Labanon to kuwa ba zai tafi haka kawai ba tare da martani mai kaushi daga wajen kungiyar ba.
-
Kasar Habasha Ta Sanar Da Shirinta Na Shiga Tsakani A Rikicin Kasar Yemen
Dec 04, 2018 17:00Firayi ministan kasar Habasha, Abiy Ahmed, ya sanar da shirin da kasarsa ta ke da shi na shiga tsakanin, tsakanin bangarorin da ba sa ga maciji a tsakaninsu a kasar Yemen don kawo karshen rikicin kasar.
-
An Bude Babban Baje Kolin Littafai Na UNESCO A Belgium
Dec 04, 2018 13:22An nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki bugun China a babban baje kolin littafai na hukumar UNESCO da ke gudana a halin yanzu.