An Bude Babban Baje Kolin Littafai Na UNESCO A Belgium
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34324-an_bude_babban_baje_kolin_littafai_na_unesco_a_belgium
An nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki bugun China a babban baje kolin littafai na hukumar UNESCO da ke gudana a halin yanzu.
(last modified 2018-12-04T13:22:17+00:00 )
Dec 04, 2018 13:22 UTC
  • An Bude Babban Baje Kolin Littafai Na UNESCO A Belgium

An nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki bugun China a babban baje kolin littafai na hukumar UNESCO da ke gudana a halin yanzu.

Kamfanin dillancin labaran Anadol ya habarta cewa, an nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki bugun China a babban baje kolin littafai na hukumar raya al’adu da tarihi ta majaliosar dinkin duniya UNESCO da ke gudana a halin yanzu a birnin Paris na kasar Faransa.

Wannan baje koli dai ya hada da littafai na tarihi da kuma wadanda aka rubuta su domin raya wasu harsuna ko al’adu na wasu al’ummo a duniya, kamar yadda aka nuna kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarkia  wurin.

Kwafin kur’anin da yafi daukar hnkali shi ne wanda aka buga a China, wanda kawata shi da rubutu kuma aka dora shi a kan dardumar Farisa wadda ake sakawa a kasar Iran.

Ana gudanar da baje kolin ne  akowace shekara, a shekaru masu za a gudanar da shi a kasashen Austria, Jamus, Turkiya, Spain, Birtaniya da kuma Amurka.