Dec 06, 2018 09:41 UTC
  • Tawagar MDD Na Neman Sojojinta 2 A Congo

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriya Demuradiyar Congo, ta ce tana neman wasu sojojinta biyu da suka bata tun a watan Nuwamba a yayin wani fada a jihar Beni dake gabashin kasar.

Sojojin dai na cikin wani aiki hadin gwiwa ne tare da sojojin kasar ta Congo, wanda tawagar MDD ta (MONUSCO) ke jagoranta,  kan 'yan tawaye (ADF), a jihar Beni dake yankin arewacin Kivu.

Tawagar ta MONUSCo dai ta ce sojoji hudu suka bata, amma an yi nasara gano guda biyu cikin koshin lafiya.

Alkalumman baya bayan nan da tawagar ta MONUSCO ta fitar sun ce sojojin na MDD bakwai ne suka mutu, a yayin da 13 suka raunana sai kuma biyu da suka bata a wata arangama data wakana a ranar 14 ga watan Nuwamba da ya gabata.

Tags