Pars Today
Ministan tsaron kasar Afganistan da kuma Babban hafsan hafsodhin kasar sun ajiye ayukansu bayan harin taliban
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi tofin Allah tsine kan harin ta'addancin da kungiyar ta'addanci ta Taliban ta kaddamar kan sojojin gwamnatin Afganistan a ranar Juma'ar da ta gabata.
Sojojin Afganistan 50 ne suka rasa rayukansu kana wasu a wani hari da kungiyar taliban ta dauki alhakin kai masu a wannan Juma'ar.
Adadin mutanen da suka mutu sakamakon amfani da wani makeken bam mafi girma da ba na nukiliya da Amurka ta yi a kasar Afghanistan sun kai mutane 94 duk kuwa da yiyuwar ci gaba da karuwar adadin saboda gagarumin karfin da bam din yake da shi.
Ma'aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ta sanar da cewa ta jefa wani makeken bam da ba na nukiliya kan wani kogo da ta ce 'yan kungiyar ta'addancin nan na ISIS suke buya a ciki a kasar Afghanistan.
Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da hallaka wani babban jigon kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Qaida mai suna Qari Yasin a wani harin jirgi marar matuki a Afganistan.
Al'umma sun wayi gari da tashin bama-bamai a garin Baglan, abin da yayi sanadiyyar rasa rayuka da dama wanda suka hada da mata da kananan yara.
Kungiyar Taliban ta ce ita ce ke da alhakin kai wasu jerin hare haren bam biyu ciki har da wanda aka dana a mota a birnin Kabul na kasar Afganistan.
Wani rahoto da tawagar MDD a Afganistan ta fitar ya nuna cewa kimanin fararen hula 11,500 ne da aka kashe ko kuma aka raunana a cikin shekara 2016 data gabata a aksar ta Afganistan.
Majiyar labarai daga kasar Afganistan sun bayyana cewa mutanen akalla biyu ne suka rasa rayukansu a lokacinda wani bom da aka dana a gefin titi ya tashi da su.