Afganistan : Taliban Ta Dau Alhakin Jerin Hare-Hare A Kabul
Mar 01, 2017 11:21 UTC
Kungiyar Taliban ta ce ita ce ke da alhakin kai wasu jerin hare haren bam biyu ciki har da wanda aka dana a mota a birnin Kabul na kasar Afganistan.
Hare haren na wannan safiyar sunyi sanadin raunanar gomman mutane a cewar wasu majiyoyin tsaron kasar.
Harin na farko dai an kai shi ne da mota a wata a wani ofishin 'yan sanda sai kuma wanda aka kai a wata cibiyar leken asiri inda mutane da dama suka raunana.
Kawo yanzu dai babu alkalumen rasa rayuka aman wasu alkaluma da ma'aikatar lafiya ta kasar ta fitar ta ce ta samu mutane 35 da suka raunana, kuma mai yiwuwa adadin zai iya karuwa.
Tags