A Afganistan Ne Aka Fi Ritsawa Da Fararen Hula A 2016
(last modified Mon, 06 Feb 2017 11:11:17 GMT )
Feb 06, 2017 11:11 UTC
  • A Afganistan Ne Aka Fi Ritsawa Da Fararen Hula A 2016

Wani rahoto da tawagar MDD a Afganistan ta fitar ya nuna cewa kimanin fararen hula 11,500 ne da aka kashe ko kuma aka raunana a cikin shekara 2016 data gabata a aksar ta Afganistan.

Wannan adadin ya sanya kasar ta farko a inda aka fi kashe fararen hula a shekara ta 2016.

A cewar kuma rahoton sama da yara 3,500 ne aka kashe sanadin rikice rikice da kasar take fama dasu na tsakanin mayaka da kuma dakarun gwamnati.

Rahoton ya ce da akwai mutane 11,500 da tashe tashen hankula ya rusa dasu da suka hada da 4,498 da suka mutu da kuma 7,920 da suka raunana.