Taliban Ta Kashe Sojojin Afganistan 50
Sojojin Afganistan 50 ne suka rasa rayukansu kana wasu a wani hari da kungiyar taliban ta dauki alhakin kai masu a wannan Juma'ar.
An dai kaiwa sojojin harin ne a yayin da suke sallar Juma'a, kamar yadda kakakin rundinar sojin Amurka a Kabul ya sanar.
Tun da farko dai wata sanarwa da ma'aikatar tsaron Afganistan din ta fitar ta ce wasu 'yan bindiga ne sanye da kakin soji suka kai harin a barikin sojin yankin Mazar-e-Sharif a arewacin kasar.
Duk dai wadanda lamarin ya rusa da su sojoji ne a cewar kakakin ma'aikatar tsaron kasar Janar Dawlat Waziri .
An dai dau lokaci mai tsawo ana ta musayar wuta da 'yan bindigan, kafin daga bisani jiragen saman sojin kasar masu saukar ungulu da kuma motocin daukar marasa lafiya su kawo dauki.
A watan Maris daya gabata kungiyar 'yan ta'addan IS ce ta dauki alhakin kai makamancin wannan harin a wani asibitin soji na Kabul inda akalla mutane hamsin suka rasa rayukansu.