-
Shugaban Kasar Venezuela Nicholas Maduro Ya yi Kakkausar Suka Ga Shuban Amurka
May 22, 2017 14:42Shugaban na kasar Venezuela ya soki Amurka da shugabanta ne saboda makarkashiyar da ta ke kitsawa kasarsa.
-
Trump Ya Isa Isra'ila A Ci Gaba Da Ran Gadinsa Na Farko
May 22, 2017 08:45A ci gaba da ran gadinsa na farko a wasu kasahen duniya, shugaban Donald Trump na Amurka ya isa Isra'ila a yau Litinin.
-
Kawo Karshen Zaman Taron Birnin Riyad Na Kasar Saudiyya Tsakanin Amurka Da Larabawa
May 22, 2017 01:47A kawo karshen zaman taro tsakanin shugaban kasar Amurka da na kasashen Larabawa da musulmi a cikin daren jiya Lahadi a birnin Riyad na Saudiyya ba tare da cimma wata matsaya kan kawo ci gaba ga kasashen na Larabawa da na musulmi ba.
-
Sharhi: Matsayin Kasar Saudiyya Wajen Cimma Siyasar Amurka A Gabas Ta Tsakiya
May 21, 2017 01:26A jiya Asabar 20, Mayun 2017 ne shugaban Amurka Donald Trump ya isa birnin Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya a ziyararsa ta farko zuwa wata kasa ta waje tun bayan da ya dare karagar mulkin kasar Amurkan.
-
Amurka Ta Kulla Yerjejeniyar Sayarwa Saudia Makamai Na Dala Billion 460
May 20, 2017 12:53Fadar white hause ta bada sanarwan cewa shugaba Donal Trump wanda a halin yanzu yake ziyarai aiki a kasra Saudia ya kulla wasu yerjeniyoyi na sayarwa ita saudia makamai wadanda suka kai dalar Amurka billion 460.
-
Amurka : Trump Zai Yi Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliyar Iran
May 18, 2017 09:40Amurka ta ce zata yi aiki da yarjejeniyar nukiliyar da mayan kasashen duniya suka cimma da Iran karkashin gwamnatin tsohon shugaba Barack Obama.
-
Bayanai Na Ci Gaba Da Fitowa Kan Dalilin Korar Shugaban FBI Da Trump Yayi
May 17, 2017 01:21Bayanai na ci gaba da fitowa dangane da dalilan da suka sanya shugaban Amurka Donald Trump ya kori shugaban Hukumar Kula Da Manyan Laifuffuka ta Amurkan (FBI) James Comey a kwanakin baya da har ya zuwa yanzu yake ci gaba da fuskantar mayar da martani.
-
Kwamitin Tsaro Zai Dauki Matakai Kan Koriya Ta Arewa
May 16, 2017 01:16Kwamitin tsaro na MDD ya yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da gwajin makamin mai linzamin da Koriya ta Arewa ta yi a baya bayan nan, tare da shan alwashin daukan kwararan matakai kan gwamnatin ta Pyongyang.
-
Amurka : Ana Zargin Trump Da Kwarmatawa Rasha Bayanai
May 16, 2017 01:15Shugaba Donald Trump na Amurka na fuskantar wani babban zargi, na cewa ya fallasawa Rasha da wasu bayanai wanda ba kasafai ake son kowa ya san da su ba.
-
Sharhi:Manufar Sarkin Saudiya Na Gayyatar Shugabani 17 Zuwa Birnin Riyad
May 13, 2017 02:15Sarkin Saudiya Salman bn Abdul-Aziz ya tura goron gayyana ga Shugabanin kasashen musulmi 17 domin su gana da Shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Riyad.