Amurka : Ana Zargin Trump Da Kwarmatawa Rasha Bayanai
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20422-amurka_ana_zargin_trump_da_kwarmatawa_rasha_bayanai
Shugaba Donald Trump na Amurka na fuskantar wani babban zargi, na cewa ya fallasawa Rasha da wasu bayanai wanda ba kasafai ake son kowa ya san da su ba.
(last modified 2018-08-22T07:00:07+00:00 )
May 16, 2017 01:15 UTC
  • Shugaba Donald Trump na Amurka
    Shugaba Donald Trump na Amurka

Shugaba Donald Trump na Amurka na fuskantar wani babban zargi, na cewa ya fallasawa Rasha da wasu bayanai wanda ba kasafai ake son kowa ya san da su ba.

Jaridar Washinton Post ta ce Mista Trump ya kwarmata bayanan ne a lokacin ganawarsa da sakataren harkokin wajen Rashar Sergio Lavror wanda ya ziyarci Amurkar a makon Jiya.

Bayanan dai sun shafi wani shiri na kungiyar IS wanda kawayen Amurka ba su so ta tattauna akansu ba da gwamnatin Moscow, wanda a cewarsu yana da matukar hadari akan musayar bayanansu da Amurkar.

Saidai shugaban kwamitin tsaron Amurkar Janar McMaster ya musunta zargin, yana mai cewa bangarorin biyu sun tattauna ne kan barazana kungiyoyin ta'addanci.

Wannan dai na zuwa ne a cikin wani yanayi na kace-nace a Amurkar, kan ko Rasha ta taka rawa a harkokin zaben shugabancin kasar, wanda ana cikin binciken ne, Trump ya kori shugaban hukumar FBI, James Comey.