Amurka Ta Kulla Yerjejeniyar Sayarwa Saudia Makamai Na Dala Billion 460
Fadar white hause ta bada sanarwan cewa shugaba Donal Trump wanda a halin yanzu yake ziyarai aiki a kasra Saudia ya kulla wasu yerjeniyoyi na sayarwa ita saudia makamai wadanda suka kai dalar Amurka billion 460.
Kamfanin dillancin Labaran Mehr na kasar Iran ya nakalto fadar white House tana fadar haka a yau Asabar ta kuma kara da cewa yerjejeniyar ta hada da makaman da Amurka zata sayarwa saudia na dalar Amurka billion 350 a cikin shekaru 10 masu zuwa, da kuma wasu na dallar Amurka 110 na yanzu yansu.
Ganin cewa a halin yanzu gwamnatin kasar saudia ta shiga yake yake da makobtanta na Yemen, Bahrai, ga kuma murkushe yan adawa a cikin gida, wannan ya nuna cewa makaman zasu kare ne a yakar wadan nan makobtanta .
Amma a bangaren shugaban kasar ta Amurka ya bayyana cewa manufar sayarwa kasar Saudia wadan nan makamai shi ne karfafa tsaron ita saudia da kuma yankin gaba daya, har'ila yau da kuma yaki da ayyukan ta'addanci.