Pars Today
Hukumar raya kogin kwara ta ABN, ta yi gargadin yiyuwar samun mummunar ambaliyar ruwa a kasashen Najeriya da Benin kasashe biyu da tafkin ke ratsawa.
Gwamnatin kasar Benin ta sanar da kawo karshen cutar zazzabin lassa da beraye ke kawowa a kasar bayan da a watan Fabrairun da ya gabata aka sanar da mutuwar mutane biyu a kasar.
Ziyarar Shugaban Kasar Benin Zuwa Najeriya
Rundunar sojin kasar Nijar ta sanar da cewa rundunar hadakar kasashen yammacin Afirka ta fara aiwatar da shirinsu na kawo karshen sauran 'yan kungiyar Boko Haram da suke kan iyakar Nijar din da Nijeriya.
Zababben shugaban kasar Benin ya sanar da cewa daga cikin abubuwan da zai aiwatar har da rage yawan shekarun wa'adin shugabanci a kasar.
Rahotanni daga kasar Jamhuriyar Benin sun bayyana cewar firayi ministan kasar kuma dan takaran jam’iyya mai mulkin a kasar Lionel Zinhou ya amince da shan kaye a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar.
A ranar Lahadi nan ce al'ummar Jamhuriyar Benin ke sake fita zuwa rumfunan zabe domin zaben shugaban kasa zagaye na biyu.
A Jamhuriyar Benin 'yan takara 24 da suka fafata a zagaye na farko na zaben shugaban kasar sun yanke shawarar marawa dan takara Patrice Talon daya zo na biyu baya a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da za'ayi a ranar 20 ga wata.
Kotun tsarin mulki a Jamhuriya Benin ta ce za'a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar inda za'a fafata tsakanin 'yan takara Lionel Zinsou da ya zo na farko da kuma Patrice Talon da ya zo na biyu.