Benin : Kotun Tsarin Mulki Ta Tantance Zaben Shugaban Kasa
(last modified Mon, 14 Mar 2016 06:28:09 GMT )
Mar 14, 2016 06:28 UTC
  • \'Yan Takara a zagaye na biyu Zinzu Da Talon
    \'Yan Takara a zagaye na biyu Zinzu Da Talon

Kotun tsarin mulki a Jamhuriya Benin ta ce za'a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar inda za'a fafata tsakanin 'yan takara Lionel Zinsou da ya zo na farko da kuma Patrice Talon da ya zo na biyu.

Hakan dai ya biyo bayan cewa babu dan takara da ya samu adadin kuri'un da ake bukata domin lashe zaben na ranar 6 ga watan Maris tun a zagayen farko.

Za'a dai je zagaye na biyu a zaben shuagabn a ranar 20 ga watan nan kamar yadda shugaban kotun tsarin mulkin kasar Théodore Holo ya sanar ga manema labarai a jiyya lahadi, tsakanin firaministan kasar mai barin gado da kuma hamshaken da kasuwan kasar Patrice Talon..

Zaben mai zuwa na ranar 20 ga wata a yayuin sa za'a zaben wanda zai maye gurbin shugaban kasar mai ci Boni Yayi da wa'adin mulkin sa ke kawo karshe a ranar biyar ga watan Afrilu mai zuwa.

Kungiyar kasashen yammacin Afrika ta CEDEAO/ECOWAS wace ta aike da masu sanya ido 120 da kwararu 16 a fadin kasar ta yaba da yadda zaben ya gudana ba tare da wasu matsaloli ba kuma cikin armashi da lumana.