Kasar Benin Ta Sanar Da Kawo Karshen Cutar Zazzabin Lassa A Kasar
Gwamnatin kasar Benin ta sanar da kawo karshen cutar zazzabin lassa da beraye ke kawowa a kasar bayan da a watan Fabrairun da ya gabata aka sanar da mutuwar mutane biyu a kasar.
Ministan kiwon lafiya na kasar Benin Dr. Alassane Seidou ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce a yau Juma'a, 14 ga watan Aprilun 2017 ina sanar da kawo karshen cutar zazzabi lassa a kasar Benin.
Ma'aikatar lafiyar kasar dai ta bayyana cewar mutane 90 din da suke da alaka da wadannan mutane biyun dai ba su nuna wata alama ta kamuwa da cutar ba tsawon kwanaki 21 da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ware, don haka gwamnatin ta sanar da kawo karshen cutar a kasar.
Cutar dai ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a Afika musamman a Nijeriya tun bayan bullar cutar a a shekara ta 2015 kamar yadda rahoton hukumar WHO din ya nuna.