Gargadin Ambaliyar Ruwa A Benin Da Nijeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23893-gargadin_ambaliyar_ruwa_a_benin_da_nijeriya
Hukumar raya kogin kwara ta ABN, ta yi gargadin yiyuwar samun mummunar ambaliyar ruwa a kasashen Najeriya da Benin kasashe biyu da tafkin ke ratsawa.
(last modified 2018-08-22T11:30:40+00:00 )
Sep 10, 2017 10:53 UTC
  • Gargadin Ambaliyar Ruwa A Benin Da Nijeriya

Hukumar raya kogin kwara ta ABN, ta yi gargadin yiyuwar samun mummunar ambaliyar ruwa a kasashen Najeriya da Benin kasashe biyu da tafkin ke ratsawa.

Wani jami'in hukumar mai suna Sungalo Kone a jamhuriya NIjar ya yi kira ga mazauna yankunan da matsalar ta shafa dasu kauracewa yakunan saboda wannan barazana.

Wannan dai na zuwa ne sakamakon ruwan saman da ake ci gaba da shatatawa tun daga watan Yuni a kasashen Mali da Nijar.

Alkalumman da hukumomi a Nijar suka fitar sun nuna cewa mutane 44 ne suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwa a Nijar.