Rundunar Hadin Gwiwa Ta Fara Aikin Kawar Da Boko Haram
(last modified Wed, 22 Jun 2016 16:14:13 GMT )
Jun 22, 2016 16:14 UTC
  • Rundunar Hadin Gwiwa Ta Fara Aikin Kawar Da Boko Haram

Rundunar sojin kasar Nijar ta sanar da cewa rundunar hadakar kasashen yammacin Afirka ta fara aiwatar da shirinsu na kawo karshen sauran 'yan kungiyar Boko Haram da suke kan iyakar Nijar din da Nijeriya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya jiyo kwamandan dakarun sojojin da aka jibge a yankin Diffa na Jamhuriyar ta Nijar, Birgediya Janar Abdou Sidikou Issa yana cewa dakarun hadakar na kasashen Nijeriya da Chadi da Nijar sun kaddamar da shirin fada da kungiyar Boko Haram da nufin yi musu kwab daya da kawo karshensu.

Shi dai wannan shirin taron dangin yana zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Boko Haram din suka kaddamar da wasu muggan hare-hare a yankin na Diffa inda suka kashe wasu sojoji da dama da kuma tilasta wa dubun dubatan mutanen yankin barin yankunan na su.

A shekarar bara ce dai kasashen Nijeriya, Nijar, Chadi, Kamaru da Benin suka cimma yarjejeniyar kafa dakarun hadakan da nufin yin kwab daya ga 'yan Boko Haram din da suka addabi kasashen na su.