Benin : Yau Ake Fafatawa Tsakanin Zinsou Da Talon A Zagaye Na biyu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2683-benin_yau_ake_fafatawa_tsakanin_zinsou_da_talon_a_zagaye_na_biyu
A ranar Lahadi nan ce al'ummar Jamhuriyar Benin ke sake fita zuwa rumfunan zabe domin zaben shugaban kasa zagaye na biyu.
(last modified 2018-08-22T11:28:00+00:00 )
Mar 20, 2016 05:16 UTC
  • wasu dake kada kuri'a a wata mazaba a Benin
    wasu dake kada kuri'a a wata mazaba a Benin

A ranar Lahadi nan ce al'ummar Jamhuriyar Benin ke sake fita zuwa rumfunan zabe domin zaben shugaban kasa zagaye na biyu.

Za'a fafata tsakanin firiministan kasar mai barin gado Lionel Zinsou da kuma hamshaken dan kasuwa na kasar Patrice Talon domin may gurbin shugaba mai barin gado Boni Yayi daka kammala wa'adin mulin sa biyu a farkon watan Afrilu mai zuwa, kamar yadda kudin tsarin mulkin kasar ya tanada.

A zagayen farko na zaben dai Lionel Zinsou ne yaza na farko da kashi 27,11% yayin da Patrice Talon ke biye masa da kashi 23,52% cikin 'yan takara 33 da suka fafata.

A zaben dai na wannan karo Mr Talon daya zo na biyu na samun goyan bayan 'yan takara 24 na zagayen farko cikin kuwa har da Sebastien Ajavon daya zo matsayi na uku na zagayen farko da kashi 22%.

shi kuwa Mr Zinsu na samun goyan bayan jam'iyya mai mulki a wannan karama kasar mai yawan al'umma data tasa miliyan 10 da dari shida, dake a yammacin Afrika.