Pars Today
A Burkina Faso an dage zaman shari'ar wadanda ake zargi da yunkurin kifar da gwamnati a watan Satumba na 2015, da aka fara a jiya Talata.
Yau Talata, an fara shari'ar wandanda ake zargi da yunkurin juyin mulki a watan Satumba na 2015 a Burkina Faso.
Shugaba Isufu Mahamadu, na Jamhuriyar Nijar ya karbi shugabancin karba-karba na kungiyar G5 ta kasashen yankin Sahel, a taron shuwagannin kungiyar karo na hudu da ya gudana jiya Talata a birnin Yamai fadar gwamnatin Nijar.
Mahukuntan Burkina Faso sun sanar da cewa: Wasu 'yan bindiga sun kai farmaki kan rundunar tsaron kasar a Gundumar Baraboule da ke kusa da kan iyaka da kasar Mali, inda suka kashe 'yan sanda biyu.
Gwamnati da kungiyoyin na ilimi a Burkina faso sun cimma ta kawo don ceto harkar harkar ilimi data tabarbare a kasar.
Masu zanga-zanga sun killace hanyoyin zuwa Jami'ar birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso wajen da shugaban kasar Faransa ke gabatar da jawabi a yau Talata lamarin da ya hana jama'a halattar taron.
Kamfanin dillancin labarun faransa ya ce an kai harin ne jim kadan bayan da shugaban kasar Faransa ya fara ziyarar aiki a cikin kasar.
Majiyar jami'an tsaro a kasar Borkina Faso ta bayyana cewa mutane biyu ne suka rasa rayukansu a yau Litinin a lokacin da wasu yan bindiga suka kai hare hare a wurare biyu a lardin Yatenga daga arewacin kasar
Majiyar jami'an tsaro kasar Borkina Faso ta bada labarin cewa wasu yan bindiga sun kai hare-hare kan jami'an tsaron kasar da suke aiki a kan iyakar kasar da kasar Mali.
A Burkina Faso, daririwan mutane ne suka gudanar da jerin gwano na neman a yi haske da kuma gurfaranar da masu hannu a kisan da akawa tsohon shugaban kasar Thomas Sankara.