Nijar : Isufu Ya Karbi Shugabancin karba-karba na G5 Sahel
Shugaba Isufu Mahamadu, na Jamhuriyar Nijar ya karbi shugabancin karba-karba na kungiyar G5 ta kasashen yankin Sahel, a taron shuwagannin kungiyar karo na hudu da ya gudana jiya Talata a birnin Yamai fadar gwamnatin Nijar.
Shugaba Ibrahim Bubakar Keita na Mali ne ya jagoranci kungiyar kafin ya mika ragamar shugabancinta ga takwaransa na Nijar.
A taron da suka gudanar Jiya, shuwagabannin sun bayyana cewa har yanzu da sauran gibi a kudaden da suke bukata wajen kaddamar da rundunar hadin gwiwa kasashen.
Shugaba Ibrahim Bubakar Keita na Mali ya fada a jawabinsa a wurin taron cewa, kawo yanzu Dala Milyan 294 kawai aka samu cikin 450 da ake bukata.
Nan gaba ne dai a ranar 23 ga watan Fabrairun nan ake sa ran kasashen biyar da suka hada da (Mali, Nijar, Chadi, Burkina Faso da Mauritania) zasu gudanar da wani taron neman tallafi a birnin Brussels.