Burkina Faso: Sojojin Faransa Uku Sun Jikkata Sanadiyyar Harba Musu Makamin Gurneti
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25831-burkina_faso_sojojin_faransa_uku_sun_jikkata_sanadiyyar_harba_musu_makamin_gurneti
Kamfanin dillancin labarun faransa ya ce an kai harin ne jim kadan bayan da shugaban kasar Faransa ya fara ziyarar aiki a cikin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:31:03+00:00 )
Nov 28, 2017 12:03 UTC
  • Burkina Faso: Sojojin Faransa Uku Sun Jikkata Sanadiyyar Harba Musu Makamin Gurneti

Kamfanin dillancin labarun faransa ya ce an kai harin ne jim kadan bayan da shugaban kasar Faransa ya fara ziyarar aiki a cikin kasar.

Majiyar tsaron kasar ta ce; wasu mutane biyu ne akan babur suka nufi inda mota mai dauke da sojojin Farasan, inda suka harba musu makami mai gurneti.

Sojojin na Faransa dai suna kan hanyarsu ne ta zuwa matsugunin shugaban kasarsu Emanuel Macron a yayin da aka kai musu harin.

Shugaba Emanuel Macron dai yana kan hanyarsa ne ta zuwa taron hadin guiwa na nahiyoyin Afirka da kuma turai  da za a yi kasar Cote De Viore, domin tattauna  hanyoyin bunkasa a laka a tsakaninsu.