Burkina : An Yi Jerin Gwanon Tunawa Da Thomas Sankara
A Burkina Faso, daririwan mutane ne suka gudanar da jerin gwano na neman a yi haske da kuma gurfaranar da masu hannu a kisan da akawa tsohon shugaban kasar Thomas Sankara.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da aka cika shekaru 30 cif da kisan da akawa Sankara a yayin juyin mulkin ranar 15 ga watan Oktoba na shekara 1987 da ya kawo tsohon amininsa Blaise Compaore a kan madafun iko.
Thomas Sankara dai soja ne mai ra'ayin 'yan mazan jiya da ya jagoranci fafutukar 'yanta kasar Burkina Faso, yana da kuma farin jini sosai ga al'ummar kasar dama mutanen Afrika da dama.
Masu jerin gwanon sanyeda fararen riguna dake dauke da hoton Sankara na raira taken neman '' Gaskiya da shari'a'' da kuma kwalaye dake dauke da ''kunya ga lalataciyyar kotu da masu shari'a''
A hannu daya kuma masu jerin gwanon sun bukaci a bude shari'a a Faransa game da batun kisan na Sankara domin zakulo yan faransa dake da hannu a kisan da a cewarsu shirya shi akayi.
A karshen watan Mayu na shekara 2015 ne aka tono gawawakin Thomas Sankara da wasu abokansa don binciken kwayoyin halitunsu don tantance musababin mutuwarsu, duk da cewa an gudanar da irin wannan binciken a kasashen Faransa da Spaniya amnan ba'a yi nasara ba.