Burkina Faso : An Cimma Matsaya Don Ceto Harkar Ilimi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27723-burkina_faso_an_cimma_matsaya_don_ceto_harkar_ilimi
Gwamnati da kungiyoyin na ilimi a Burkina faso sun cimma ta kawo don ceto harkar harkar ilimi data tabarbare a kasar.
(last modified 2018-08-22T11:31:21+00:00 )
Jan 28, 2018 18:00 UTC
  • Burkina Faso : An Cimma Matsaya Don Ceto Harkar Ilimi

Gwamnati da kungiyoyin na ilimi a Burkina faso sun cimma ta kawo don ceto harkar harkar ilimi data tabarbare a kasar.

An dai shafe kusan wattani hudu kungiyoyin malumai da daliban makarantun boko ke yajin aiki a wannan kasar.

kakakin kungiyar maluman makarantu ta kasar, Wendyam Zongo, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren Faransa na AFP cewa sun cimma matsaya da gwamnati cewa zata kara kaso a harkar ilimi a cikin kasafin kudi na kasar a cikin shekaru masu zuwa.

Kana kuma gwamnatin ta amunce shafewa bangarorin hawaye, ciki har da inganta yanayin aikinsu, sannan zata samar da hanyoyin fitar daliban jami'a waje don ci gaba da karatu da kuma samar da wuraren kwara ga dalibai.