-
Koriya Ta Arewa Ta Ce Babu Ja Da Baya Dangane Da Shirin Makamanta Masu Linzami
Aug 23, 2017 05:27Kasar Koriya ta Arewa ta bayyana cewar babu batun ja da baya ko cimma wata yarjejeniya dangane da shirinta na ci gaba da karfafa makamanta masu linzami ba.
-
Donald Trump: Shugaban Koriya Ta Arewa Mutum Ne Mai Hikima
Aug 17, 2017 06:45Bayan kwashe tsawon watanni ana cacar baki da ma barazanar kai wa juna hari da manyan makamai a tsakanin gwamnatin Amurka da kuma Koriya ta arewa, shugaban kasar ta Amurka ya fito ya jinjina wa shugaban kasar Koriya ta arewa, tare da bayyana shi mutum mai hikima, sakamakon dakatar da harba makamai masu linzami da kasarsa ta shirya yi a kusa da tsibirin Guam.
-
MDD Ta Bayyana Aniyarta Na Magance Rikicin Koriya Da Ya Kunno Kai
Aug 17, 2017 05:37Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewar rikicin da a halin yanzu ya kunno kai a tsibirin Koriya wani rikici ne maras tamka tsawon shekarun da suka gabata, don haka MDD a shirye take ta shigo don magance rikicin.
-
Pyongyang Ta Soke Shirin Harba Makami Mai Linzami Zuwa Amurka
Aug 15, 2017 06:24Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya ce ya dan tsaida shirinsa na harba makami mai linzami zuwa tsibirin Guam na Amurka dake yankin Pacifique.
-
Rasha Ta Damu Kan Rikicin Amurka Da Koriya Ta Arewa
Aug 11, 2017 15:07Kasar Rasha ta ce ta damu sosai akan rikicin kasashen Amurka da Koriya ta Arewa, wanda ta ce akwai barazana ta yin amfani da karfi sosai a cikin rikicin.
-
Koria Ta Arewa Ta Yi Watsi Da Barazanar Trump Sannan Ta Bayyana Shirin Kaiwa Sojojin Amurka Hari A Guam
Aug 10, 2017 06:46Gwamtanin koriya ta Arewa ta yi watsi da barazanar shugaban Amurka Donal Trump na barin wutan da duniya bata taba gani ba a kanta, ta kuma kara fayyace shirinta ta cilla makaman masu linzami kan sansanin sojojin Amurka mafi girma na Guam a kasar Japan.
-
Trump: Koriya Ta Arewa Za Ta Fuskanci Matsananci Fushi Daga Amurka
Aug 09, 2017 16:38Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa, idan Koriya ta arewa ta ci gab ada yin barazana a kan Amurka, to tabbas za ta fuskanci fushi da wuta daga Amurka, da duniya bata taba ganin irinsu.
-
Trump : Ban Lamunta Da Yadda China Ba Ta Tsawatawa Koriya Ta Arewa Ba
Jul 30, 2017 06:20Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce ba zai lamunta ko kadan ba da yadda kasar China bata daukar wani ba mataki ba kan Koriya ta Arewa.
-
EU Ta Damu Kan Kakabawa Rasha Takunkumi
Jul 26, 2017 15:51Kungiyar tarayya turai ta nuna damuwa akan sabbin takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar Rasha.
-
China Ta Nuna Adawa Na Daukan Matakin Soja A Kan Kasar Koriya Ta Arewa
Jul 06, 2017 06:29Wakilin China a MDD ya nuna adawa dangane da daukar matakin Soja kan kasar Koriya ta Arewa.