Rasha Ta Damu Kan Rikicin Amurka Da Koriya Ta Arewa
(last modified Fri, 11 Aug 2017 15:07:27 GMT )
Aug 11, 2017 15:07 UTC
  • Rasha Ta Damu Kan Rikicin Amurka Da Koriya Ta Arewa

Kasar Rasha ta ce ta damu sosai akan rikicin kasashen Amurka da Koriya ta Arewa, wanda ta ce akwai barazana ta yin amfani da karfi sosai a cikin rikicin.

Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha Sergueï Lavrov wanda ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da matasa da aka watsa kai tsaye a gidan talabijin din kasar, ya ce mahukuntan Washington ne ya kamata su sassauto kan matsayinsu domin kaucewa fadawa wani babban rikici.

Mista Lavrov ya kara da cewa kasarsa zata yi iya kokarinta na ganin cewa ba'a kai ga fafatawa ba tsakanin kasashen biyu.

Ya kuma kara da tunatar da cewa mahukuntan Peken da Moscow sun sha gabatar da shawarwari na ganin an kai zuciya nesa tsakanin Amurkar da Koriya ta Arewa, ta hanyar cewa bangarorin biyu su daina duk wani shirin tsokana irin na harba makamai masu linzami da na nukiliya na koriya ta Arewa da kuma atisayan soji da hadin gwiwar sojojin kasashen Amurka da Koriya ta Kudu.

Ko a wannan Juma'a ma shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar yin amfani da karfi kan Koriya ta Arewa, inda ya ce matakin soji kan kasar na nan daram.