-
Masar Da Habasha Za Su Warware Takaddamar Da Ke Tsakaninsu
Apr 20, 2017 13:17Mahukuntan masar da Habasha sun jadda cewa za su shawo kan matsalolin da ke tsakaninsu da suke da alaka da batun gina katafariyar madatsar ruwa ta al-nahdah da kasar ta Habasha ke yi, inda Masar ke ganin hakan a matsayin wata babbar matsala a gare ta.
-
Yansanda A Kasar Masar Sun Kashe Mutumin Da Ake Tuhuma Da Kai Hari Kusa Da Wani Coki A Kasar
Apr 20, 2017 10:33Majiyar yan sanda a kasar Masar ta bayyana cewa yansandan sun kashe wani mutum wanda ake tsammani yana da hannu a cikin harin ta'addanci da aka kai a kusa da wani coci a yankin Sina wanda ya kai ga mutuwar dansada guda da kuma raunata wasu ukku.
-
Jami'an Tsaron Masar Sun Kama Wasu Gungun 'Yan Ta'adda A Yankunan Kasar
Apr 17, 2017 01:18Jami'an tsaron Masar sun yi nasarar kama wasu gungun 'yan ta'adda da suke shirye-shiryen kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan cibiyoyin gwamnati da wajajen bautan mabiya addinin Kirista a kasar.
-
Tsiraru Kiristoci A Masar Suna Gudanar Da Bukukuwan Esta Cikin Zullumi Da Tsoro
Apr 16, 2017 14:42Kiridtoci tsiraru a kasar Masar suna gudanar da bukukuwan Ester a cikin fargaba bayan harin ta'addancin da ya halaka mutane 45 a ranar Lahadin da ta gabata
-
Masar : An Daure Tsohon Minista Shekara 7 A Gidan Yari
Apr 15, 2017 10:12Wata Kotu a Masar ta yankewa tsohon ministan cikin gidan kasar, Habib al-Adly, hukuncin zamen gidan yari na shekara bakwai bisa samunsa da laifin cin hanci da rashawa.
-
Masar Ta Bukaci Hadin Kan Duniya A Fagen Warware Rikici Da Tashe-Tashen Hankula
Apr 13, 2017 06:45Ministan harkokin wajen kasar Masar ya bayyana cewa: Matsalolin ayyukan ta'addanci da rikici da suke ci gaba da addabar al'ummomi suna bukatar hadin kan duniya domin samun nasarar warware su.
-
Masar : An Tantance Maharin Cocin Alexandri
Apr 13, 2017 01:24Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar ta ce ta gano mutumin da ake zargin shine ya shirya harin kunar bakin wake wanda ya kashe kansa a cocin KIfdawa ta Saint Mark a Alexandria, harin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 17.
-
Masar Ta yi Suka Ga Kasashen Da Su Ke Kare 'Yan ta'adda.
Apr 12, 2017 14:32Pira ministan Masar Sharif Isma'ila ya ce; Harin ta'addanci na karshe da aka kai a kasar da akwai hannun wasu kasashen waje.
-
Majalisar Dokokin Masar Ta Amince Da Kafa Dokar Ta Baci A Kasar
Apr 11, 2017 14:31Majalisar dokokin kasar Masar ta amince da kafa doka ta baci a kasar na tsawon wattannin ukku bayan harin ta'addancin da aka kai kan wasu wuraren bauta na kiristoci a ranar lahadin da ta gabata.
-
Majalisar Dokokin Masar Ta Amince Da Bukatar Yin Gyarar Fuska Dokar Yaki Da Ta'addanci A Kasar
Apr 11, 2017 05:54Majalisar Dokokin Masar ta kada kuri'ar amincewa da daftarin kudurin neman aiwatar da gyare-gyare a dokokin da suka shafi yaki da ayyukan ta'addanci a kasar.